Connect with us

News

Sojoji Sun Yi Wa ’Yan Bindiga Ruwan Wuta A Kaduna

Published

on

Daga Kabiru Basiru Fulatan

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar kashe ’yan bindiga da dama a wani samame da suka kai yankin Galbi da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna

Advertisement

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

A cewar Aruwan, rundunar Operation Forest Sanity tare da hadin gwiwar sojojin sama suka far wa matattarar ’yan bindiga a yankin na Galbi.

Advertisement

Salman Rushdie ya farfaɗo bayan kai masa harin wuka a Amurka

Duk da cewa kwamishinan bai bayyana adadin ’yan bindigan da aka kashe ba, amma ya ce dakarun sun samu nasarar kwace bindigogi masu sarrafa kan su guda biyu da kuma AK47 guda uku da babura bakwai.

Advertisement

Ya bayyana cewa, tun da farko dakarun sun tsallaka Kogin Kaduna inda suka rika musayar wuta da ’yan bindigar, bayan haka ne suka samu kashe da dama daga cikinsu.

Sanarwar ta ce Gwamnatin Kaduna ta gode wa sojojin kasa da na sama da ’yan sanda da jami’an tattara bayanan sirri da ’yan bijilanti da wadanda suka taimaka wurin samun wannan nasara.

Advertisement

Aruwan ya kuma bukaci jami’an tsaron da su kara kaimi wajen fatattakar ‘yan ta’addan da suka samu mafaka a wasu dazukan da sauran maboyar ’yan bindigar da aka gano a fadin jihar.

 

Advertisement

 

DAILY TRUST

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending