News
Yan bindinga sunyi garkuwa da mutane biyu garin katsina
Daga Muslim yunus Abdullahi
A jiya ne dai da yammacin ranar asabar wasu yan bindinga sukayi garkuwa da wasu mutane guda biyu agarin Yan Daka dake karamar Hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Lamarin yafarune da misalin karfe hudu na Rana ne dai Yan bindinga suka shiga garin kimanin awa biyu suna cin karansu ba babbaka kamar yanda mazaunin garin yabaiyana muna
Sojoji Sun Yi Wa ’Yan Bindiga Ruwan Wuta A Kaduna
Ya kara da cewa bayan su tarasu aguri daya sai suka zabi mutum biyu wato da wani magidanci da kuma wata matar aure guda daya suka yi garkuwa dasu
Yace tafiyarsu ke da wuya sai suka aike musu da sakon cewa baza su saki mutanen ba har sai an kai musu Naira Million Bakwai amatsayin kudin fansa
yace su dai mutanen wannan Garin suna fama fa rashin tsaro. Inda yace su dai mutanan wannan yakin sun fara tunanin su kamar ba Yan Nigeria bane Amma sunce su yanzu sun maida lamarinsu ga Allah
ya kara da cewa suna rokon gwamnatin jiha da kuma ta gwamnatin taraiyya da ta dubi al’ummar wannan yankin da idon Rahma da a taimakesu akawo masu dauki domin yanzu yakai kusan kullum sai Yan ta’adda sun kai musu Hari
