News
Sai Mun Binciko Duk Mai Hannu A Kisan Sheikh Aisami— Gwamna Buni
Daga: Hamza Yusuf Abdulmumin
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, a ranar Lahadin, ya bayyana alhininsa kan kisan da aka yi wa Sheikh Goni Aisami, wani malamin addinin Islama da ke garin Gashua a karamar hukumar Bade ta jihar.
Jaridar Dimokuradiyya, A ranar Juma’a ne wasu sojoji biyu suka harbe Aisami a Jaji-Maji, karamar hukumar Karasuwa ta jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, ya ce an kama sojojin da suka yi yunkurin sace motar marigayin kuma za a gurfanar da su a gaban kuliya.
The Punch ta nakalto cewa, Buni, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Damaturu ta hannun babban daraktan yada labaransa da hulda da manema labarai, Alhaji Mamman Mohammed, ya bayyana halin da ake ciki na kisan a matsayin abin bakin ciki, da abin takaici
Lamarin da ake zargin ya shafi mutuwar, abin takaici ne kuma za a yi bincike sosai.
“Gwamnati za ta tabbatar da cewa an binciki kowane bayani dalla-dalla kuma duk wanda aka samu da hannu , zai fuskanci fushin doka.
“Gwamnatin jihar za ta yi aiki kafada da kafada da jami’an tsaro don bankado duk wani bayani dalla-dalla don tabbatar da an yi adalci kan kisan Shehin Malamin” inji shi.
Kamfanin Dillancin Labarai Na kasa NAN ya ruwaito cewa, Gwamnan ya jajantawa iyalan mamacin da al’ummar karamar hukumar Bade da ma na jihar baki daya bisa rasuwar Aisami.
Buni ya yi kira gare su da su kwantar da hankulansu kuma su bi doka saboda ana ci gaba da gudanar da bincike kuma za a ci gaba da bin diddiginsa lamarin har zuwa karshen.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan marigayin ya kuma baiwa iyalansa da daukacin al’ummar jihar hakurin jure rashin sa.
Nguru Reporters
