News
2023: Ni zan karbi mulkin Kano a hannun gwamna Ganduje — Sha’aban Sharada
Daga Yasir sani abdullahi
Dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar ADP a kakar zaben shekarar 2023 mai zuwa, dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Birni, Sha’aban Ibrahim Sharada, yace da yardar Allah shi ne wanda zai karbi mulkin jihar Kano a hannun gwamna Abdullahi Umar Ganduje a zaben shekarar 2023.
Sha’aban Sharada yace yaso ace shi ne zai yiwa jam’iyyar APC takarar gwamnan Kano, sai dai kuma Allah bai nufa ba, amma shi hakan ma alheri ya zamo masa, domin ya samu tikiti a ADP, jam’iyya mai taken “Alheri” dabi’ar da Annabi ya umarci al’umma su runguma.
Cikin jawaban da ya gabatar, Sharada yace ya sauya sheƙa ne saboda rashin adalci da jam’iyyarsa ta APC ta yi masa wanda kuma bai ji dadin abubuwan da suka faru ba, shi yasa ya koma ADP kuma yana fatan zai ci zabe kafin 12 na rana.
