Connect with us

News

Sojoji sun kubutar da tsohuwa da wasu mutum biyu a Birnin Gwari

Published

on

Sojoji

Daga Usman Abdullahi jibirin

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kubutar da wasu mutum uku da aka sace a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Advertisement

Rundunar ta ce jami’anta da ke aiki a karkashin runduna ta daya ne suka ceto mutanen daga hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da su a kauyen Manini da ke Birnin Gwari a ranar Alhamis.

‘Yan bindigar da suka sace mutanen sun yi musayar wuta sosai da sojojin lamarin da ya sa wasun su suka samu raunuka sannan suka arce cikin daji suka bar wadanda suka sata in ji rundunar.

Advertisement

Mutanen da aka ceto sun hada da maza biyu da kuma wata tsohuwa.

Tuni dai sojojin suka kai su cikin Kaduna in da ake duba lafiyarsu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending