Connect with us

News

Zaben 2023: Jonathan ya nemi ‘yan siyasar Najeriya su rika taka-tsantsan

Published

on

Goodluck Jonathan

Daga Idris Hussain Nguru

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya bukaci ‘yan takara da kuma sauran ‘yan siyasa a kan su rika taka-tsantsan a kan dorewar kasa da kuma sanya jin dadi da walwalar al’ummar kasar a gaba a yayin yaki neman zabe.

Advertisement

Goodluck Jonathan, ya yi wannan kira ne a ranar Alhamis a wajen taron shekara-shekara kan irin tariin da tsohon shugaban mulkin sojan kasar Ibrahim Badamasi Babangida ya kafa.

A cewarsa, yana da matukar muhimmanci ga ‘yan Najeriya su kawar da dukkan wasu bambance-bambancen da ke tsakaninsu, su shiga a dama da su a cikin harkokin siyasa don zabar shugabannin da za su kawo sauyi a kasar.

Advertisement

Ya ce,” Zabuka masu zuwa suna da matukar muhimmanci wajen ci gaban mu, a don haka ne nake jan hankalin ‘yan siyasa da su rinka taka-tsantsan wajen hada kai da kuma samar da zaman lafiya a kasa.”

Jonathan, ya ce a wannan lokaci da ake ciki bai kamata mu rinka nuna halin ko in kula da abubuwa da suka dace mu mayar da hankali a kai ba, dole mu sanya a ran mu cewa zamu shiga a dama damu a cikin harkokin siyasa.Dole kuma mu wayar wa da sauran ‘yan uwanmu kai a kan muhimmancin kada kuri’a a lokacin zabe.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending