News
An kama matar da ta sayar da jaririnta a kan N600,000 a Ogun
Daga Kabiru basiru fulatan
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun da ke kudancin Najeriya ta tabbatar da kama wata mata mai kimanin shekara 23 da haihuwa da zargin sayar da jaririnta dan kimanin makonni uku da haihuwa.
Rundunar ta ce ta kama matar mai suna, Mary Olatayo, ne bayan mahaifin jaririn ya kai mata korafi a kai.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce mahaifin jaririn ya shaida musu cewa Mary ta samu juna biyu tare da shi to a nan ne ya kama mata gida ta zauna har ta haihu.
Ya ce, bayan ta haifi danta namiji da makonni uku sai ya nemeta ya rasa ta gudu da jaririn.
Mutumin ya ce bai tashi ganin ta ba sai a wani otel in da ta ke harkokinta da maza, amma kuma ba bu jariri.
Daga nan ne sai mutumin ya kai korafi ofishin ‘yan sanda aka tura aka kamata, bayan an kai ta ofishin ‘yan sandan ne aka tuhumeta sosai a nan ne ta bayanna cewa ta sayar da jaririn ga wani a Anambra a kan kudi naira dubu dari shida.
Ta shaida wa ‘yan sandan cewa wata kawarta ce Chioma Ogbonna, ta kai ta wajen wanda ta sayar wa da jaririn a Anambra kuma tuni suka raba kudin tare.
Bincike ya gano cewa Mary, wadda ‘yar asalin jihar Kwara ce taje aiki ne a Ogun, kuma ko da taga ta samu da, sai take gani kamar zai kawo mata cikas a harkokinta shi ya sa ma ta yanke shawarar kawar da shi kawai.
Tuni dai aka tuntubi mutumin da aka sayar wa da jaririn don ya dawo da shi.
