News
An dakatar da matuƙa jirgin sama saboda bai wa hammata iska a sararin samaniya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rikici ya ɓarke cikin jirgi tsakanin wasu matuƙa jirgin samaImage caption: Rikici ya ɓarke cikin jirgi tsakanin wasu matuƙa jirgin sama
Rahotanni na cewa an sallami wasu matuƙa jirgin saman kamfain Air-France biyu sakamakon gwada ƙwanji da suka yi cikin jirgi.
’Yan Daba Sun Kone Gidan ’Yan Shi’a A Kano
Matuƙin jirgin da mataimakinsa sun ba hammata iska yayin da suke tuƙa jirgi ƙirar Airbus A320 daga Geneva zuwa Paris a watan Yuni kamar yadda jaridar Swiss News Outlet ta shaida.
Ma’aikatan jirgin sun shiga tsakani inda ɗaya daga cikin ma’aikatan ya tsaya tare da matuƙa jirgin har sai da jirgin ya sauka ba tare da matsala ba.
Faɗan nasu dai bai shafi sufurin jirgin ba, a cewar kamfanin jirgin.
Lamarin kuma ya faru ne bayan wallafa wani rahoto da hukumar da ke bincike kan sufurin jiragen sama ta Faransa ta yi ranar Talata da ya ce kamfanin jirgin yana sako-sako game da tsare-tsarensa na tsaro.
-
News6 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News5 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
-
News6 days ago
Musa Illiyasu Kwankwaso Ya Taya Sanata Lado Murnar Cika Shekaru 60, Ya Kira Shi Gogaggen Ɗan Siyasa

