Connect with us

News

Ɗan Afirka ta Kudu ya yi gudun kilomita 90 sabo da soyayya

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAH 

 

 

 

 

 

Advertisement

Wani ɗan Afirka ta Kudu da ya yi wata bajinta don kawai ya tabbatar da soyayyarsa ga masoyiyarsa ya ja hankalin masu amfani da shafukan sada zumunta.

Mutumin mai shekara 57, mai suna Joseph Kagiso Ndlovu, ya yi gudun kilomita 90 a wata gasar tsere ta ultra-marathon domin kawai ya nemi amincewar masoyiysarsa, Prudence.

 

An dakatar da matuƙa jirgin sama saboda bai wa hammata iska a sararin samaniya

An nuna shi riƙe da wata tuta inda a jiki aka rubuta saƙon da ke neman matar ta amince ta aure shi dai-dai lokacin da ya ke dab da kammala tseren.

“Prudence, za ki aure ni? Na yi gudun kilomita 90 saboda ke,” kamar yadda aka rubuta.

Advertisement

Kafafen yada labaran ƙasar da kuma wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi ta tsokaci kan labarin mutumin da ya yi wannan bajinta saboda so.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending