Fadar shugaban Najeriya ta karyata zargin da gwamnan jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya ya yi na cewa wani babban jami’in tsaro ya shaida masa cewa shugaba Buhari ne ya hana jami’an tsaro kama fulani makiyayan da ke da hannu a tashin hankala da jihar ke fuskanta.
Yadda Na Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU A Kwana Daya – Jonathan
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar ya ce wannan ikirarin da gwamnan ya yi babu kanshin gaskiya a cikinsa. idan kuma gwamnan ta tabbatar da ikirarin nasa to ya fito karara ya bayyana sunan jami’in tsaron da ya sanar da shi wannan batu, in kuwa ba haka ba to ya yi shiru da bakinsu, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sanarwar ta ci gaba da cewa a daidai wannan lokaci da matsalar tsaro ke kara ta’azzara, ya kamata ‘yan siyasa su yi kokarin hada kan jama’a, a maimakon yin kalaman da za su wargaza hadin kan al’umar kasa
