News
Tekun Sindh a Pakistan na kokarin ballewa sabowa ruwan sama
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Mahukunta a kudancin Pakistan na ta fadi tashin ganin sun kare babban tekun yankin daga ballewa saboda kada ruwa ya cinye garuruwa da ke kusa da shi.
Ministan lardin Sindh ya ce yawan ruwan da ke tekun ya kai ba a iya ganin karshensa kuma yana neman ya balle duk da tare shin da aka yi.
Yajin aikin malaman ASUU ka iya janyo babbar masifa ga Najeriya’
A yanzu ana ci gaba da kiraye kirayen yadda za a samar da abubuwan da za su tare ruwan.
Tuni dai daruruwan mazauna kauyukan da ke kusa da kogin suka koma garuruwa makwabta. Fiye da mutane 1300 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan da ta afkawa kasar.
Ana ta kiraye-kirayen a sake yi wa tekun hanyoyin da ruwan zai wuce, a daidai lokacin da ya kara tumbatsa, sakamakon hadewa da kogin Indus.
Daruruwan mazauna kauyuka mafi kusa na ta kwashe komatsansu domin kaura zuwa garuruwa makofta kamar su Sehwan, domin tsira daga bala’in ambaliyar ruwa.
Sama da mutane 1,300 ambliyar ta hallaka a Pakistan a watan da ya gabata, lokacin da aka shafe makonni ana sheka ruwan sama a kasar
