News
Masu garkuwa da mutane sun bukaci kudin fansa domin sakin matafiya a Ondo
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Masu garkuwa da mutane da suka kama matafiya a hanyar Benin zuwa Ondo, sun bukaci a biya naira miliyan 90 domin sakin matafiyan.
Gidan Talabijin na Channel Tv a Najeriya ya ruwaito kwamishiniyar yada labaran jihar Ondo Mrs Bamidele Ademola- Olateju na bayyana hakan ga manema labarai.
Mutum 372 Sun Mutu Sakamakon Ambaliyar Ruwa —NEMA
Ta kara da cewa ya zuwa yanzu fasinjoji 18 ne ke hannun masu garkuwar, a yayin da tara suka kubuta.
A ranar Asabar ne dai aka kama matafiyan a kan hanyarsu ta komawa Ondo bayan wata jana’iza da suka halarta a bienin Benin jihar Edo.
BBC NEWS
Advertisements
