News
EFCC ta gurfanar da kakakin majalisar dokokin jihar Ogun a gaban kotu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar da ke yaki da cin hanci da karbar rashawa ta Najeriya EFCC ta gurfanar da kakakin majalisar dokokin jihar Ogun Olakunle Oluomo a gaban wata babbar kotun tarayya da ke jihar Legas, bisa laifin sama da fadi na kudi sama da naira biliyan 2.5
Masu garkuwa da mutane sun bukaci kudin fansa domin sakin matafiya a Ondo
Gidan talabijin na Channels Tv a Najeriya ya ruwaito cewa an gurfanar da kakakin tare da daraktan kudi na majalisar dokokin jihar Oladayo Samuel, da kuma Akawun majalisar Adeyemo Taiwo.
Ana yi musu tuhuma 11 da suka hadar da hadin baki, da satar kudi da bayar da bayanan bogi, zargin da dukkansu suka musanta.
Advertisements
