News
‘Yan Nigeria da dama za su yi arziki a wannan shekara – Masanin tattalin arzikin Duniya.
Daga kabiru basiru fulatan
Fitaccen masanin tattalin arzikin Duniya, ‘Bismarck Rewane’ ya ce, ‘yan Nigeria da dama za su yi arziki a wannan shekara ta 2022.
Masanin tattalin arzikin yayi wannan hasashe ne a wajen wani taro da cibiyar kula da kasuwanci tsakanin Nigeria da Burtaniya ta shirya a Lagos.
Ya ce bangaren ICT kasuwancin da baya alaka da man fetur zai samu tagomashi mai yawa.
A cewar sa tattalin arzikin Nigeria zai bunkasa da kaso uku da digo hudu ( 3.4) a wannan shekara.
“Ba ko shakka wannan shekara za ta zamo alheri ga ‘yan Nigeria, inda al’ummar kasar kudu da arewa za su samu arziki wanda shine mafi girma da alfanu ga kasar cikin shekaru da dama da suka gabata” A cewar Bismarck Rewane.
Me za su kace kan wannan hasashe da fitaccen masanin tattalin arzikin ya yi?
-
News5 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
News6 days ago
An Tura Kwamishinonin ’Yansanda 30 Da Jami’ai 15,000 Domin Sanya Ido A Zaɓen Osun
-
News3 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
