News
Gwamnan Kwara ya naɗa Inyamiri da Bafulatani a matsayin mataimaka na musamman
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
AbdulRahman AbdulRazaq, gwamnan jihar Kwara, ya naɗa wani ɗan kabilar Igbo, Chukwugozie Igwebuike, da Mohammed Abdullahi, Bafullatani a matsayin mataimaka na musamman kan hulɗa tsakanin al’umma.
Rafiu Ajakaye, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan, a cikin wata sanarwa a jiya Talata, ya ce yayin da aka nada Chukwugozie a matsayin mataimaki na musamman (Igbo), shi ma Abdullahi an nada shi a matsayin mataimaki na musamman (Fulani).
Ajakaye ya kuma ce an naɗa ɗan jarida, Abdulateef Kolawole a matsayin mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Gwamnan jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq ya amince da nadin sabbin mataimaka na musamman guda uku, ciki har da biyu kan huldar jama’a da zurfafa hada kai a sassa daban-daban na jihar.
“Yayin da aka nada Chukwugozie Angus Igwebuike mataimaki na musamman ga gwamna kan hulda da jama’a (Igbo), an nada Muhammed Abdullahi a matsayin mataimaki na musamman kan huldar tsakanin al’ummomin (Fulani).
“Dukkan biyun shugabannin al’umma ne da ake mutuntawa, kasancewar sun zauna a jihar Kwara tsawon shekaru.
“Gwamnan, a halin yanzu, ya nada wani matashin dan jarida, mai fafutukar ci gaban matasa, da kuma kwararren masanin sadarwa Ibraheem Abdullateef Kolawole a matsayin mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa.
“Dan shekara 27, Abdullateef, wanda aka fi sani da Egghead saboda hazakarsa, a halin yanzu dan majalisar matasan Najeriya ne inda yake wakiltar mazabar Kwara ta tsakiya. Shi ne wanda ya kafa Raise, dandali da yake hada kai da sauran Matasa Turkawa don azurta matasa su zama masu dogaro da kai da kuma sa ido.”
Daily Nigerian Hausa
