News
NDLEA ta kama ƙwayoyin Tramadol guda miliyan 13 a Legas
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Hukumar da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya wato NDLEA ta kai samame wani gidan alfarma a Unguwar Lekki a Legas inda ta ce ta gano miyagun ƙwayoyi.
Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ne ya bayyana haka a shafinsa na Twitter inda ya ce an gano ƙwayoyin Tramadol guda miliyan 13 a gidan .
Ƴar shekara 3 ta rasu bayan da wani magidanci yai mata fyaɗe a Kano
Ya bayyana cewa duka ƙwayoyin suna nauyin miligram 225.
Mista Femi ya bayyana cewa gidan babu wani bil adama da ke zaune a ciki, sai dai waɗannan ƙwayoyi da aka ajiye a ciki.
Ya kuma ce tuni aka kama wanda ake zargi da ajiye ƙwayoyin inda a halin yanzu yake hannun NDLEA.
A ƴan kwanakin nan dai hukumar ta NDLEA na wawan kamu inda ko a kwanakin baya sai da ta kama hodar ibilis ta biliyoyin naira da kuma dubban kwalaben A-Kurkura da tabar wiwi a samame daban-daban da ta kai a fadin Najeriya.
BBC
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
