Connect with us

News

Gwamnatin Kogi ta yi ikirarin mallakar kamfanin siminti na Obajana kuma ta fara yunkurin ƙwato shi daga hannun Dangote

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

A ranar Alhamis ne gwamnatin Kogi ta fara ɗaukar gaɓaran ƙwato kamfanin siminti na Obajana daga hannun kamfanin siminti na Dangote.

Advertisement

 

Kudurin gwamnatin na kunshe ne a cikin rahoton kwamitin kwararru na musamman don tabbatar da halascin mallakar kamfanin siminti na Obajana zuwa na Dangote.

Advertisement

Saba Dokokin Hanya: Kotu Ta Hukunta Mutum 35 A Edo

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa an mika cikakken rahoton ga gwamna Yahaya Bello na Kogi a watan Satumba.

Advertisement

 

Sakatariyar gwamnatin jihar (SSG), Folashade Ayoade ce ta gabatar da rahoton a ranar Alhamis a Lokoja.

Advertisement

 

Ayoade ta ce, ” ƙwato kamfanin siminti na Obajana Plc daga kamfanin Dangote Cement Company Limited ya zama wajibi a wannan lokaci.”

Advertisement

 

SSG ɗin ta gabatar da takardu cewa maida Obajana zuwa ga kamfanin Dangote “Ba halastacce ba, kuma rusasshe ne”.

Advertisement

 

Ta bayyana cewa a cikin rahoton, an nuna yadda a ka yi amfani da amfani da takaddun mallaka guda 3 na Kamfanin Simintin Obajana, mallakin gwamnatin Jihar Kogi, inda Dangote ya yi amfani da hakan ya ciyo bashin Naira biliyan 63bn.

Advertisement

 

A cewarta, kwamitin bisa ga binciken da ya gudanar, ya bayar da shawarar cewa jihar Kogi ta dauki matakin kwato kamfanin siminti na Obajana daga hannun Dangote.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending