Connect with us

News

Biyan kudin haraji zai rage wa Najeriya basussukan da ake bin ta – Ministar Kudi

Published

on

ZAINAB_AHMED

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Ministar kudi, kasafi da kuma tsare-tsare ta Najeriya, Zainab Shamsuna Ahmed, ta ce hanyar da ta dace na ragewa kasar ɗimbin basuka da ake bin ta shine biyan kudin haraji da kuma shawo kan matsaloli da ake samu na kudaden shiga.

Zainab ta bayyana hakan ne jiya Talata a Abuja, a wurin taron ƙarawa juna sani kan yadda ake kashe kudaden haraji da kungiyar ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma ECOWAS ta shirya.

Advertisement

Buhari ya umurci ministoci su fara shirya bayanai na miƙa mulki

Jaridar Daily Trust  ta ruwaito cewa an kuma shirya taron ne kan bijiro da tsare-tsare na yadda za a yi amfani da kudaden haraji da kuma sanya ido kan miƙa bayanai kan kudin tsakaninn mambobin kasashen ECOWAS.

Advertisement

Ministar wacce ta samu wakilcin wata babbar darekta a ma’aikatar, Fatima Hayatu, ta ce gwamnati ta dmau matuka kan yadda ake kashe kudaden haraji.

Idan za a iya tunawa dai, a watan Yuli ne, gwamnati ta sanar da cewa bashin da ake bin kasar ya zuwa zangon farko na wannan shekarar ya kai naira tiriliyan 1.94 wanda kuma ya zarta yawan kudaden shiga da aka samu na naira biliyan 310 a lokacin, inda hakan ya nuna cewa basukan da ake bin Najeriyar ya zarta kudaden shiga da take samu a yanzu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending