News
Buhari ya bukaci ‘yan sanda su zama ‘yan ba ruwana a zaben 2023
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci jami’an ‘yan sandan ƙasar da su zama ‘yan ba ruwana tare da da bijiro da shirye-shirye da za su taimakawa waje ganin an samu sahihin sakamako a zabukan 2023 da ke tafe a fadin ƙasar.
Buhari ya bayyana hakan ne a yau Litinin yayin wani bikin ƙarawa juna sani na kwana uku da aka shiryawa manyan jami’an ‘yan sandan ƙasar domin duba matsalolin barazanar tsaro da ake fuskanta wadanda kuma ake ganin za su kawo cikas a zabukan.
Masu motocin bos na haya sun fara yajin aiki a Legas
Da yake tabbatar musu da cikakkiyar goyon bayansa gabanin zabukan na 2023, Buhari ya nuna jin dadinsa kan irin sauye-sauye da aka samu a karkashinsa wadanda kuma ke kawo ci gaba musaman ta yadda ‘yan sanda ke gudanar da ayyukansu cikin korewa yanda doka ta tanada.
”A don haka therefore, na hori sufeto janar na ‘yan sanda da ya tabbatar da cewa an bai wa kowane dan kasa dama da kuma hakkinsa na zabar wanda yake so kamar yanda tsarin mulki ya tanada, domin kuma ganin cewa sakamakon zabe ya kasance zabin mutane,” in ji Buhari.
Shugaban ya kuma kara nanata zimmar sa na ganin an gudanar da zabuka masu tsafta cike kuma da gaskiya a shekara ta 2023.
Shi ma da yake magana, gwamnan jihar ta Imo, Hope Uzodinma, ya yi kira ga ‘yan sandan ƙasar da su kawo tsare-tsare na wajabtawa ‘yan ƙasar shan rantsuwar cewa ba za su tayar da tarzoma ba lokacin gudanar da zabe.
Da yake mayar da martani, Sufeton yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya tabbatar wa shugaban da ‘yan Najeriya cewa rundunar za ta yi aiki wajen ganin zabukan na 2023 sun tafi yadda ya kamata ta hanyar bijiro da tsare-tsare kan sha’anin tsaro da kuma kyautata yanayin siyasa a ƙasar.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
