News
Donald trump ya zargi sabuwar gwamnatin america da Bata masa suna
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Donald Trump ya miƙa buƙatar gaggawa ga Kotun Ƙolin Amurka da ke neman ta hana kwamitin Majalisar Dokokin ƙasar mai rinjayen ‘yan Dimokrat, samun bayanan dukiyar da ya kamata ya biya wa haraji.
Mai Martaba Sarkin Dosso ya rasu yana da shekara 99
A makon jiya, wata kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukunce-hukunce guda biyu na ƙaramar kotu da ke umartar tsohon shugaban ƙasar ya ba su bayanan dukiyar tasa.
Lauyoyin Mista Trump sun ce gaskiyar dalilan da suka sa ake neman bayanan harajinsa ita ce neman ɓata shi a siyasance, daidai lokacin da yake neman sake tsayawa takarar shugaban ƙasa.
Kwamitin Majalisar Dokokin mai ƙarfin faɗa-a-ji na neman bin diddigin kuɗaɗen harajinsa tun bayan da ya zama shugaban ƙasa na farko a cikin shekara 40 da ya ƙi fitar da irin waɗannan bayanai bainar jama’a.
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
