News
Matsalolin da masana’antu ke haifarwa a fanin sauyin yanayi na karuwa matuka
DAGA MUHAMAD MUHAMAD ZAHRADDIN
Wani sabon bincike da aka gudanar ya nuna cewa tasirin masana’antu ko bangarorin da ke cin moriyar makamashi mai gurbata muhalli ya karu sosai a shekarun nan.
Nazarin wanda kungiyar yaƙi da sauyin yanayi ta Global Witness, ta yi ya nuna cewa sama da mutane 600 da ke halartar taron koli na sauyin yanayi na duniya a Masar, suna da alaƙa da kamfanonin mai da gas.
Yan Daba Sun Kona Ofishin INEC Na Ogun
Bayanan da rahoton ya kunsa wadanda aka nuna wa BBC, sun nuna cewa masu kamun kafa na irin wadannan kamfanoni har ma sun fi yawan wakilan kasashen da ke fama da matsalar sauyin yanayi da suka hada da Pakistan da Bangladesh da Mozambique a taron.
Masu fafutuka sun ce nan gaba suna son a haramta wa wakilan irin wadannan kamfanoni halartar duk wani taron koli na sauyin yanayi
