Connect with us

News

Gobara Ta Kashe Mutum 90 A Kaduna A Wata 9

Published

on

Yan kwana-kwana na kashe gobarar Bangledash

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Mutum 90 sun rasu, wasu 76 sun jikkata sakamakon gobara a Jihar Kaduna a cikin wata tara na farkon shekarar 2022 da muke ciki.

 

Advertisement

Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA) ta ce an samu gobara sau 436 daga watan Janairu zuwa Satumba a fadin jihar.

 

Advertisement

Ronaldo zai jagoranci tawagar Portugal a gasar Kofin Duniya 

Da yake jawabi a taron wayar da kan jama’ar jihar kan gobara, Kodinetan Shiyyar Arewa maso Yamma na Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Imam Garki, ya ce yawancin gobara da ake samu, dan Adam ne ke haddasawa.

Advertisement

 

Don haka ya yi kira gare su da su rika daukar matakan hana tashinta a kowane lokaci.

Advertisement

 

Aminiya ta rawaito cewa   wayar da kan al’umma a wannan lokaci na da muhimmanci ganin cewa hunturu, wanda shi ne lokacin aka fi samun gobara, ya kara matsawo.

Advertisement

 

“NEMA, a matsayin ja-gaba a kasa waje yaki da bala’o’i, tana wayar da kan gwamnatocin jihohi da hukumomi da daidaikun mutane kan matakan da suka fi dacewa su dauka,” in ji shi.

Advertisement

 

Taron wayar da kan wani bangare ne na taron kara wa juna sani na kwana uku da hadin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta Kasa da kuma Christian Aid/COOPI.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending