News
Gobara Ta Kashe Mutum 90 A Kaduna A Wata 9
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mutum 90 sun rasu, wasu 76 sun jikkata sakamakon gobara a Jihar Kaduna a cikin wata tara na farkon shekarar 2022 da muke ciki.
Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA) ta ce an samu gobara sau 436 daga watan Janairu zuwa Satumba a fadin jihar.
Ronaldo zai jagoranci tawagar Portugal a gasar Kofin Duniya
Da yake jawabi a taron wayar da kan jama’ar jihar kan gobara, Kodinetan Shiyyar Arewa maso Yamma na Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Imam Garki, ya ce yawancin gobara da ake samu, dan Adam ne ke haddasawa.
Don haka ya yi kira gare su da su rika daukar matakan hana tashinta a kowane lokaci.
Aminiya ta rawaito cewa wayar da kan al’umma a wannan lokaci na da muhimmanci ganin cewa hunturu, wanda shi ne lokacin aka fi samun gobara, ya kara matsawo.
“NEMA, a matsayin ja-gaba a kasa waje yaki da bala’o’i, tana wayar da kan gwamnatocin jihohi da hukumomi da daidaikun mutane kan matakan da suka fi dacewa su dauka,” in ji shi.
Taron wayar da kan wani bangare ne na taron kara wa juna sani na kwana uku da hadin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta Kasa da kuma Christian Aid/COOPI.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News5 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
