News
Za A Kara Wa Abuja Megawatt 800 Na Lantarki
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shirye-shirye sun yi nisa na kara inganta hanyoyin samar da wutar lantarki a Abuja da kewaye.
Ministan Makamashi, Abubakar Aliyu, ya ce aikin zai kara karfin wutar lanatarkin da kamfanin TCN ke samarwa a yankin da megawats 1,000.
Ministan ya ce, Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kasa (TCN) ne ya ke aikin wanda aka yi masa lakabi da ‘Aikin Zoben Abuja’.
Ya kuma ce, kungiyar taimaka wa kasashe ta gwamnatin Faransa (AFD) ce ta dauki nauyin aikin da aljihunta.
Aminiya ta rawaito cewa Ana sa rai aikin zai samar da karin karfin lantarki wanda za a kara wa tasoshin wutar lantarki na Dawaki da Apo da Kuje da Lugbe da kuma Wumba, wanda za a kaddamar a watan disamba.
Ya sanar da hakan yayin da yake jawabi ga ’yan jarida bayan ziyarar gani da ido da ya kai wurin aikin samar da wutar lantarki ga birnin a ranar Juma’a.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
