News
Malaman addini a Sudan na zanga-zanga kan sabon kundin tsarin mulkin ƙasar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Dubban malaman addini sun cika titunan Sudan a karo na biyu cikin mako biyu domin zanga-zangar kin amincewa da tsoma bakin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a tattaunawar da ake yi kan mika mulki hannun farar hula.
Har yanzu ƙungiyoyin addinai na goyon bayan tsohon shugaban kasar da aka hambarar Omar al-Bashir, inda suka yi watsi da daftarin kundin tsarin mulki da kungiyar lauyoyin Sudan ta gabatar.
Cikin daftarin, za a haramta ayyukan jam’iyyar NCP ta Mista Bashir. MDD ta shiga tattaunawa tsakanin gwamnatin sojin kasar da haɗakar farar hula, da zimmar tsayar da lokacin zaɓe da zai mika kasar ga farar hula.
A makon da ya wuce malaman sun yi irin wannan zanga-zangar a wajen ofishin MDD da ke birnin Khartoum.
Advertisements
