News
Najeriya na da isassun kudaden da za ta kula da kowane dan kasa. – Kwankwaso
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), Rabiu Kwankwaso, ya ce Najeriya na da isassun kudaden da za ta kula da kowane dan kasa.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi kan rancen kudi wanda ya kawo koma baya ga tattalin arzikin kasar nan a shekarun baya a yayin taron ‘The People’s Townhall 2023, wanda gidan talabijin na Channels ya shirya kai tsaye a Abuja a yammacin Lahadi.
Da Yawan Mukarraban Gwamnatin Buhari Kamata Yayi Ace Suna Kurkuku – SDP
Tsohon gwamnan jihar Kano wanda ya ce ya biya duk basussukan da ya ci karo da su a matsayinsa na gwamna a Kano ba tare da ya ci bashi ba.
Ya ce, “Akwai kudi da yawa a kasar nan, duk wanda ya ce babu kudi ko dai bai sani ba ko kuma yana son yin barna. Akwai isassun kudaden da za su kula da kowannenmu a kasar nan; mun yi shi a Kano a 1999 zuwa 2003, mun ci bashi da yawa, mun biya bashin bayan shekara takwas. Lokacin da na koma na ci karo da basussukan daruruwan miliyoyin dalar Amurka, kuma mun daidaita su kafin in tafi a shekarar 2015.
“Ina maganar karbar kudi ko dai daga bankuna ko kuma daidaikun mutane, ba mu taba rance ba. Don haka na yi imanin cewa za a iya kwaikwayi hakan sosai a matakin kasa. Ba zan ce ba zan yi rance ba amma idan abubuwa ne masu muhimmanci su biya kansu, ba wai su ci bashi don biyan albashi ba, kula da kudaden da ake kashewa a halin yanzu da sauransu, na yi imanin cewa akwai ma isashen kudi a kasar nan da za a iya gudanar da hakan.”
Kwankwaso ya kuma ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa zai tattauna da masu karbar bashi na Najeriya don sake jadawalin biyan basussuka domin gwamnati ta samu kudin da za ta kula da wasu abubuwa.
“Halin da ake gaya mana a yanzu shi ne, duk abin da muke samu a matsayin albarkatunmu, kasancewar kudadenmu a kasar nan ba su isa su biya mana bashin da ake bin mu ba, ina ganin abin da muka ji kenan. Yanzu maganar ita ce, duk ranar da gwamnati ta dauki nauyinta za ta zauna da daukacin jama’a, masu ba da lamuni, su ga yadda za a sake tsara su, dole ne a yi shawarwari.
“Ba za ku iya tattara duk abin da kuka samu ba kuna biyan ruwa ga masu ba da lamuni, dole ne a shirya don tabbatar da cewa an ba ku sararin numfashi ta yadda za ku fara kawo abubuwan da suka dace don ci gaban kasa. ” ya kara da cewa
