Connect with us

News

‘Yan Majalisar Dokokin Nijar Sun Musanta Zargin Kara Wa Kansu Kudaden Alawus

Published

on

Yan Majalisun dokokin niger

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Tun a tsakiyar watan Nuwamban 2022 ne dambarwa akan yunkurin kara wa ‘yan majalisar dokokin kasar Nijar  ta kudaden alawus-alawus ta kunno kai. Yayin da wasu ke ganin dacewar matakin a bisa dalilai na inganta  rayuwar wakilan al’umma wasu kuwa na nuna rashin amincewarsu da abinda suke kira hanyar kara wa kasa larura a wani lokaci da ake cikin mawuyacin hali, wannan ne dalilin da ya sa majalisar ta yi zama a ranar Laraba domin fayyace sassan da ta yi wa gyaran fuska a dokar biyan kudaden alawus din

Advertisement

 

yan majalisa, kamar yadda Honorable Kalla Moutari, shugaban kwamitin ‘yan majalisa mai kula da sha’anin doka ya bayyana.

Advertisement

 

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 8 A Kauyen Filato

Advertisement

 

Ta hanyar wannan zama majalisar na kokarin wanke kanta daga zargin da take fuskanta, dalilin da ya sa ra’ayoyi suka zo daya a tsakanin ‘yan majalisar masu rinjaye da na adawa game da wannan magana ta gyaran fuskar dokar kudaden alawus. Kamar yadda VOA HAUSA ta rawaito

Advertisement

 

Aikin dan majalisa wani abu ne da ya ta’allaka kan maganar kare hakkokin jama’ar kasa,  da sanin muhimmancin wannan matsayin ne ya sa ‘yan majalisar dokokin Nijar ke da mafi karancin albashi idan aka kwatanta da takwarorin aikinsu na kasashen yammacin Afrika, inji Honorable Boukari Sani Zilly.

Advertisement

 

Sabon tsarin biyan kudaden alawus-alawus din da aka yi mahawara a kansa ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba ya sami amincewar dukkan ‘yan majalisa 151 da suka halarci zauren majalisar kafin a nan gaba a gabatar wa bangaren zartarwa  kudirin don tabbatar da shi a matsayin doka ko kuma a maido da shi don sake yi masa karatu na biyu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending