Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 8 A Kauyen Filato

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Yan bindiga sun kashe mutum takwas yayin wani hari na daren ranar Talata da suka kai kauyen Wumat da ke Karamar Hukumar Bokkos a Jihar Filato.

 

Advertisement

Wani mazaunin kauyen mai suna Adamu Isa ya shaida wa Aminiya cewa, ‘yan bindigar sun kai farmakin ne da misalin karfe 10 na dare, inda suka fara harbe-harbe don tarwatsa masu kai komo, wanda a sanadiyar haka ajali ya katse hanzarin mutanen takwas.

 

Advertisement

Ba zai yiwu mu ci gaba da aikin rajistar zaɓe ba – INEC

Isa ya ce “Yawan wadanda suka mutu zai iya haura takwas saboda an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

 

Advertisement

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya ce ba shi da masaniya kan aukuwar harin sai dai ya ce zai binciki lamarin.

 

Advertisement

Harin na baya-bayan nan dai na zuwa ne kwanaki bakwai bayan da wasu ‘yan bindiga suka kashe mutane 11 tare da raunata wasu a unguwar Maikatako da ke Karamar Hukumar Bokkos a jihar ta Filato.

 

Advertisement

Jihar Filato na ci gaba da fama da fadace-fadacen kabilanci da kuma ayyukan ’yan bindiga da bata-gari.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending