Connect with us

News

Mayakan Ansaru Sun Kashe ’Yan Bindiga Biyar A Kaduna

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

’Yan bindiga biyar sun yi gamo da karshensu yayin wata arangama da suka yi da ’ya’yan kungiyar Ansaru a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

Advertisement

 

Wasu mazauna garin Damarin sun shaida wa Muryar Amurka cewa, a daren Litinin din makon nan ne dai ’yan kungiyar Ansarun suka kashe ’yan bindiga biyar.

Advertisement

 

2023: Ko Babu Goyon Bayan Wike Za Mu Lashe Zabe —PDP

Mutanen wadanda su ka nemi a sakaya sunan su bisa dalilan tsaro, sun ce suna fama da hare-haren ’yan-bindiga a yankin sosai sai dai idan ’yan kungiyar Ansaru sun shigo garin sukan ba su kariya.

Advertisement

 

Dama dai yankin Damarin karamar hukumar Birnin Gwari na fama da hare-haren ‘yan-bindiga na tsawon lokaci sai dai wasu al’ummar garin sun ce duk lokacin da ’yan kungiyar Ansaru su ka je garin ‘yan bindigan ba sa samun damar satar mutane da dukiyarsu.

Advertisement

 

Masana harkokin tsaro irin su Manjo Yahaya Shinko mai ritaya dai na garin cewa akwai bukatar daukar matakan gaggawa game da karbuwar ’yan kungiyar Ansaru a gurin al’ummomin yankunan Birnin Gwari don gudun abun da ka iya biyo baya.

Advertisement

 

Ya ce matukar dai gwamnati ba ta gaggauta daukar matakan magance matsalar tsaro a yankin ba al’ummomi za su ci gaba da daukaka ’yan kungiyar ta Ansaru tunda suke kare su.

Advertisement

 

Labarin bayyanar ’yan kungiyar Ansaru a wasu yankunan Jihar Kaduna dai ya dade sai dai Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna Samuel Aruwan ya ce gwamnati na aiki tukuru kan maganar matsalar tsaro a jihar baki daya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending