Connect with us

News

Gwamnati ta amince a fara amfani da harshen Hausa wajen koyar da ‘yan firamare

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ta amince da Dokar Harshe ta Ƙasa wadda ta ba da damar koyar da harshen uwa a makarantun firamare a faɗin ƙasa.

 

Advertisement

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya bayyana wa manema labarai hakan bayan kammala taron mako-makon da Majalisar ta saba shiryawa ranar Laraba a Abuja.Ya ce da samuwar wannan doka, hakan na nufin daga yanzu da harshen uwa za a riƙa koyar da ‘yan firamare daga aji ɗaya zuwa shida.

 

Advertisement

Ya ƙara da cewa, yanzu wannan mataki ya samu shiga tsare-tsaren gwamnati amma zai ɗauki lokaci kafin ɗabbaƙa shi.Wannan mataki in ji ministan, ana buƙatar ya shafi harsunan da ake da su a faɗin ƙasar.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending