News
an fara gwajin rigakafin Ebola a Uganda
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Uganda ta karɓi rigakafin cutar Ebola guda 1,200 wadda za a yi amfani da ita domin kariya daga nau’in cutar wadda ta samo asali daga Sudan.
Ya zuwa yanzu dai babu rigakafin da aka tabbatar tana aiki kan irin wannan nau’in cutar.
Kotu Ta Ci Maigadi Tarar N530,000 Kan Satar Na’urar Dumama Ruwa
An samu mutum 142 da suka kamu da cutar, yayin da 55 suka mutu tun bayan ɓallewar cutar a watan Satumba.
Za a bayar da rigakafin ne ga mutane waɗanda suka yi mu’amala da waɗanda suka kamu da cutar.
Masu binciken na sa ran mutum 3,000 ne za su shiga gwajin.
Akwai ƙorafin cewa an kawo rigakafin ne a ƙurarren lokaci.
Advertisements
