News
Hukumar NDLEA ta kama masu safarar mggan kwayoyi 23,907 cikin watanni 22 a Najeriya
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA, ta sanar da kwace sama da kwayar maganin Tramadol miliyan 100, cikin watanni 22 a sassa daban-daban na kasar.
Shugaban hukumar Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya ne ya sanar da hakana aranar Talata a wurin taron raba kyautuka da karin girma ga wasu daga cikin ma’aikatan hukumar a Abuja babban birnin Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta ambato Marwa na cewa ”Cikin watanni 22, hukumarmu ta kama masu safarar mutane 23,907, ciki har da shugabanninsu 29. Mun kuma kama sama da tan 5,500 na muggan kwayoyi, da suka kai darajar naira biliyan 450.
Matakin da muka dauka, na samame gida-gida da ake shuka ganyen tabar wiwi, ya ba mu nasarar lalata eka 772.5 na gonakin wiwi. Mun kuma yi nasara ba ‘yar kadan ba wajen rage yaduwar muggan kwayoyi, da sabuntawa wadanda sukai nisa a shaye-shayen tunani,” in ji Marwa.
Marwa ya ce idan har wadannan muggan kwayoyi suka fada hannun bata gari, Allah ne kadai ya san abin da zai faru idan kwayoyin suka fada hannun jama’a musamman matasa.
Ba wannan ne lokacin farko da NDLEA ke yin irin wannan wawan kamun na miyagun kwayoyi, sai dai har yanzu ana fama da matsalar shaye-shaye ba ga matasa da magidanta ba, har da mata da kananan yara a Najeriya.
