Connect with us

News

An gano gawa 213 ciki har da sojoji 10 a karanbattarsu da ‘yan bindiga a Zamfara

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

An gano gawawwaki 213 da suka hada da ‘yan ta’adda da masu kai musu bayanai, kwanaki kadan da mummunar musayar wutar da aka yi tsakanin sojojin Najeriya da ‘yan bindigar a wasu yankunan jihar Zamfara.

 

Advertisement

Jaridar PRNigeria ta rawaito, sojoji 10 na daga cikin wadanda suka mutu a lokacin da ‘yan bindigar suka fantsama garuruwan da ke kusa.

Ummita: Rashin Shaida Ya Kawo Tsaiko A Shari’ar Dan China

A ranar Litinin ma PRNigeria ta rawaito dakarun rundunar Operation Hadarin Daji sun yi nasara kan ‘yan bindigar a kauyen Malele da ke karamar hukumar Dansadau a jihar Zamfara.

Advertisement

 

Samame ta sama da sojojin sama na Najeriyar suka kai a ranar Asabar ya yi nasarar hallaka gwamman ‘yan fashin dajin ciki har da wasu manya daga cikinsu.

Advertisement

 

An samu karuwar hare-haren ‘yan ta’adda a jihar Zamfara, sakamakon yadda sojojin Najeriya ke fatattakarsu daga inda suke buya, samamen da aka kai garuruwan Malele, Maigoge, Yan Sawayu, Ruwan Tofa, Mai Awaki, and Zama Lafiya, da ke karkashin gundumar Mutunji a karamar hukumar Dansadau sun kara kai mi.

Advertisement

 

‘Yan fashin daji da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da zama babbar barazana a jihar Zamfara, inda suke haddasa rasa rayuka da dukiya, ko da yake gwamnatin jihar da jami’an tsaro na cewa su na bakin kokarin magance matsalar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending