Connect with us

News

Sojojin Najeriya sun fatattaki gungun ‘yan ta’adda a Zurmi

Published

on

Jirgin yakin Najeriya

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Rahotanni daga yankin arewa maso yammacin Najeriya sun ce rundunar sojin saman Najeriya, ta yi nasarar fatattakar gungun ‘yan ta’adda a yankin Zurmi da ke jihar Zamfara.

 

Advertisement

 

Yayin harin da dakarun Najeriya suka kai a ranar Asabar, sun samu nasarar kashe ‘yan bindiga 16 daga cikin gungun da suka tarwatsa, sai dai jagoransu da yayi kaurin suna wajen ta’addanci mai suna Dankarami, da aka fi sani da Gwaska ya tsallake rijiya da baya tare da munanan raunuka.

Advertisement

2023: Amurka Za Ta Mara Wa Najeriya Baya A Harkar Zabe

Kafar watsa labarai ta Intanet ta PRNigeria, ta ruwaito wata majiya na cewa gabanin farmakin jiragen yakin Najeriyar, kasurgumin dan ta’adddan ya yi ta kokawa kan kudurin sojojin Najeriya na kawar da shi da iyalansa.

 

Advertisement

Bayanai sun ce sai da jiragen yakin Najeriya suka shafe sa’o’i suna ruwan bama bamai kan sansanin Dankarami, kamar yadda kakakin rundunar sojin saman Najeriya Edward Gabkwet, ya tabbatar.

 

Advertisement

Dankarami da aka fi sani da Gwaska dan asalin karamar hukumar Zurmi a Zamfara, wanda ya yi kaurin suna wajen ta’addanci a yankunan arewacin jihar ta sa da kuma yankunan yammacin jihar Katsina.

 

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending