Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Rufe ‘Wellcare’ Kan Kin Karbar Tsoffin Kudi

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta ba da umarnin rufe shagon zamani na Wellcare nan take kan kin karbar tsoffin takardun Naira da aka sauya wa fasali daga hannun kwastomomi.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya umarci Shugaban Hukumar Kare Hakkin Masu Sayayya ta Jihar Kano, Baffa Dan’agundi, ya gaggauta rufe katafaren shagon da ke garin Kano ne a ranar Asabar.

Advertisement

Wata Mai Juna Biyu Ta Rasa Ranta sakamakon Ƙarancin Takardun Kuɗi

Bayan rufe Wellcare, Dan’aguni ya ce gwamnatin jihar za ta dauki matakin shari’a a kan Wellcare.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar ba ta haramta amfani da tsoffin takardun kudin ba, kuma duk  dan kasuwar da ta samu yana kin karbar su, zai yaba wa aya zabi.

Advertisement

Wasu majiyoyi sun ce tuni kamfanin Wellcare Alliance Limited, suka aike da takardar neman afuwa ga Gwamna Gwanduje da kuma rokon ya ba da izinin sake bude shagon nasu da aka rufe.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending