Connect with us

News

Wata mata a kano ta nemi mijinta ya  sake ta don  ya hana ta  kudin birthday.

Published

on

An maka wata sabuwar amarya mai suna Fatima Bashir da akafi sani da yar Albarka   a kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Post Office, Kano bisa  kwaraya wa mijinta Alhaji Nura Gambo ruwan sanyi don ya ki ba ta kudin da za ta gudanar da bikin ‘birthday’ dinta.

Wannan mataki na wannan amarya, ya sa mijin ya fara makyarkyatar sanyi, da ya kamu da rashin lafiya.

Advertisement

Kotu Ta Yanke Wa Malami Daurin Rai-Da-Rai Kan Yi Wa Yarinya Fyade

‘Yan sanda da dai ne suka gurfanar da ‘Yar Albarka a gaban Alkali Nazifi Adam kan zargin keta hakkin dan’Adam da kuma tsoratarwa.

Lauyan mijin Badamasi Gandu, ya fada wa kotun cewa matar ta nemi mijin ya ba ta wasu kudi domin bikin zagayowar ranar haihuwarta, shi kuma ya ki ba ta, shi ne dalilin da ya sa ta nemi illata shi, kuma ta nemi ya sake ta.

Advertisement

Lauyaj ya sanar da kotun cewa idan har tana son ya sake ta, dole sai ta biya shi diyyar kudi Naira milyan 10 da ya kashe wajen aurensu.

Dcl hausa ta rawaito cewa amaryar ta ki amsa laifinta, kotu kuma ta bayar da ita beli kan sharadin cewa har yanzu matarsa ce, sai kotun ta dage zaman sauraron karar zuwa ranar 3 ga Maris, 2023.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending