Connect with us

News

Sauya Fasalin Naira: Gwamnonin APC 3 Sun Gana Da Ministan Malami.

Published

on

 

 

Advertisement

Gwamnonin jam’iyyar APC guda uku a ranar Litinin din nan sun gana da ministan shari’a, Abubakar Malami da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, kan manufar musanya Naira.

 

Advertisement

Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa taron ya dauki kusan awa daya ana gudanar da shi a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa a ranar Litinin din nan.

 

Advertisement

Wadanda suka halarci taron sun hada da Gwamnan Kaduna mai barin gado Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, Yahaya Bello na jihar Kogi da Bello Matawalle na jihar Zamfara.

Rundunar Yan sanda sun kama mutum 27 kan zargin tashin hankali a Shagamu

Taron na zuwa ne gabanin zaman da kotun koli za ta yi ranar Laraba kan shari’ar da ke tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnoni uku.

Advertisement

 

Idan dai za a iya tunawa, gwamnonin ukun da suka fusata sun maka gwamnatin tarayya a gaban kotu, inda suka bukaci a dakatar da ci gaba da aiwatar da manufofin sake fasalin Naira na CBN.

Advertisement

 

Sai dai kotun kolin ta dage sauraron karar zuwa ranar 22 ga watan Fabrairu.

Advertisement

 

Babu labari har kawo yanzu kan ainihin abun da suka cimma a yayin zaman, amma da dukkan alamu ba zai wuce shirye shiryen da suke domin tunkarar hukuncin kotun koli ba a ranar Laraba mai zuwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending