News
DSS Ta Tsananta Binciken Emefiele Kan Daukar Nauyin Ta’addanci
Hukumar tsaro ta DSS ta tsananta bincike a kan Gwmanan Babban Bankin Najeriya (CBN) domin gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin almundahana da daukar nauyin kungiyar ta’addanci ta IPOB.
Aminiya ta gano haka ne a yayin da wasu rahotanni ke zargin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya da bai wa Emefiele kariya a gida da kuma ofishinsa, domin hana a kama shi, zargin da Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta musanta.
Mawakin Hausa G fresh ya gurfana a gaban Hukumar Hisbah kan zargin wasa da Sallah
Bayan yunkurin DSS na tsare Gwamnan CBN din a baya ya faskara, hukumar ta bi wasu sabbin hanyoyi tare da tsananta bincike a kansa ka zage-zagen da ake masa.
A baya-bayan nan kafar yada labarai ta Premium Times ta walla wasu bayanai na musamman da ta samu daga kotu kan dambarwar Emefiele.
Takardar kotun ta nuna ana zargin Gwmanan CBN din da daukar nauyin ’yan bindiga da kuma ayyukan kungiyar ’yan ta’addan IPOB.
Rahoton ya kuma zargi Emefiele da yin zagon kasa ga Gwamnatin Shugaba Buhari, daukar nauyin ta’addanci wasu abubuwa da ke barazana ga tsaron Najeriya.
Ana kuma zargin sa da karkatar da Bankin NIRSAL da ke karkashin CBN da kuma shirin noma na Anchor Borrower da CBN ke kula da shi.
Ana kuma zargin Gwmanan na CBN da daukar nauyin reshen soji na kungiyar IPOB, wato ESN, ta hanyar amfani da kudaden sata da kuma da ya yi amfani da su wajen neman takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC, wanda Bola Tinubu ya lashe zaben fidda gwanin.
Tuni dai Gwamnatin Tarayya ta ayyana IPOB a matsayin Kungiyar ta’addanci.
IPOB dai kungiya ce da ke neman ballewa daga Najeriya, kuma ta dade tana kai miyagun hare-haren kan cibiyoyin gwamnati tare da kashe mutane, musmman jami’an tsaro.
Maharan IPOB sun kuma kashe faraten hula da dama, tare da kakaba wa mazauna yankunan Kudu maso Gabashin Najeriya zaman gida a ranakun Litinin.
A baya-bayan nan dai IPOB ta tsananta kai hare-hare a kan ofishin ’yan sanda, inda take kashe jami’ai ta sace makamai, sai kuma ofisoshin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), inda suke kona kayayyakin zabe.
