Politics
Atiku ne Ya Tarwatsa Jam’iyyar PDP – Kiyamo
Kakakin kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC,PCC, Festus Keyamo, ya bayyana yadda jam’iyyar PDP ta lalata kanta da kanta.
Keyamo ya ce rashin kishin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya taimaka wajen ruguza jam’iyyar adawar.
Yace Ya lura cewa gazawar PDP na bude tikitin takarar shugaban kasa a 2023 zuwa dukkan sassan kasar “ya ruguza” jam’iyyar.
Bayan haka, Atiku ya fito a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam,iyyar PDP inda ya doke Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom a zaben fidda gwani na shugaban kasa.
Sai dai Keyamo ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: “Yanzu za a iya cewa gazawar PDP wajen mutunta tsarin shiyya-shiyya na kasa da kuma rashin kishin Atiku, ya lalata PDP cikin sauki.”
Atiku ya sha kaye a hannun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na ranar Asabar da ta gabata.
