Real Betis da Real Madrid za su buga wasan mako na 24 ranar Lahadi a gasar La Liga a filin wasa na Benito Villamarin.
Ranar 3 ga watan Satumba Real ta ci Betis 2-1 a filin wasa na Santiago Bernabeu, kuma Vinicius da Rodrygo ne suka ci mata kwallaye.
Yayin da Betis ta zare daya ta hannun Sergio Canales.
Real Madrid tana mataki na biyu a teburin La Liga da tazarar maki takwas tsakaninta da Barcelona ta daya mai maki 59.
Ita kuwa Betis mai maki 40 tana ta biyar a teburi da tazarar maki 12 tsakaninta da Real Madrid.
Bayan da Real ta bayyana ‘yan kwallon da za su kara da Betis daga baya ta bayar da sanarwar cewar Álvaro Odriozola ba zai buga fafatawar ba, wanda zai yi jinya.
Tuni Carlos Ancelotti ya sanar da ‘yan wasan Real da ya je da su Betis don buga karawar:
