Connect with us

Sports

Manchester United Ta Tankado Keyar Barcelona Daga Europa

Published

on

Manchester United ta tankado keyar Barcelona yayin da ta samu gurbin ’yan 16 da za su ci gaba da buga gasar Europa League.

Hakan dai ya faru ne bayan da United ta yi nasara a kan Barcelona ranar Alhamis a Old Trafford.

Advertisement

Manoma dama sauran Al,ummar najeriya sun yi shirin futowa domin su cinciba Alhaji Atiku Abubakar zuwa kan karagar Mulki 2023.

United ta yi nasarar cin kungiyar Nou Camp 2-1 a wasa na biyu a gurbin kai wa matakin ’yan 16 a Karamar Gasar ta Zakarun Turai.

Barcelona ce ta fara cin kwallo ta hannun Robert Lewandowski a minti na 18 a bugun fenariti.

Advertisement

Kwallo na 25 da ya ci wa Barcelona kenan a wasa 30 a dukkan karawa a bana, karo na 12 a jere da yake zura kwallo 25 ko fiye da haka a kakar tamaula.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Fred ya farke, sannan Anthony ya kara na biyu.

Advertisement

Anthony ya canji Weghorst – United ta zura kwallo 19 daga dan wasan da ya yi canji a kakar nan a dukkan fafatawa, ba wadda ta kaita amfana da hakan a manyan gasar Turai biyar.

Manchester United wadda ta buga 2-2 a makon jiya a Nou Camp, ta kai zagayen gaba da cin kwallo 4-3 gida da waje kenan.

Advertisement

Wasa na 15 da aka kara tsakanin kungiyoyin biyu kenan, inda United ta yi nasara a hudu da canjaras biyar Barcelona ta ci shida.

United wadda take takarar lashe kofi hudu a bana, za ta buga wasan karshe a Wembley da Newcastle United a Caraboa Cup ranar Lahadi.

Advertisement

Ranar Lahadi, Barcelona wadda take ta daya a teburin La Liga da tazarar maki takwas tsakaninta da Real Madrid, za ta ziyarci Almeria a wasan mako na 23.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending