Connect with us

News

Haramun Ne Tsawwalla Farashin Kayan Masarufi Lokacin Ramadan” Nasihar Shugaba Buhari Ga Yan Kasuwa

Published

on

 

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce al’adar kara farashin kayan masarufi da yan kasuwa ke yi lokacin azumin watan Ramadan ya saba da koyarwar addini.

Advertisement

Shugaban ya bayyana haka ne ranar Laraba lokacin da ya ke taya al’ummar musulmi murnar zagayowar watan azumin Ramadan.

Jihohi shida da suka koma hannun ƴan adawa a Najeriya

A sakon na fatan alheri don bikin fara gudanar da azumin wata mai alfarma na Ramadan, shugaban ya bukaci musulmi da su yi amfani da watan ”don aikata kyawawan ayyukan musulunci, da kuma kaucewa zunubi.”

Advertisement

A wata sanarwa ta hannun mai taimaka masa a fannin yada labarai, Mallam Garba Shehu, shugaba Buhari ya ce: ”Bari mu yi amfani da wannan damar don aikata kyawawan ayyukan koyarwar addinin musulunci, kamar kyautatawa da taimakon dan Adam.”

Shugaban ya cigaba da cewa, ”Wannan babbar dama ce ta komawa ga Allah da kuma gujewa shedancin da zai cutar da al’umma.”

Advertisement

Buhari ya ce: ”Ramadan lokaci ne da ake kauracewa ci da sha daga fitowar rana zuwa faduwarta, wanda ke janyo talaka da mai kudi su dandana irin yanayi guda, don karfafa alaka tsakanin ma su kudi da marasa kudi.”

Shugaba Buhari ya ce: ”A yayin da mu ka fara azumin kwana 30, mu tuna cewa Ramadan ba lokaci ne na kauracewa ci da sha kadai ba, lokaci ne na kauracewa duk wani shedanci da rashin kyautatawa da ke cutar da al’umma.

Advertisement

Ina sane da irin halayyar da wasu yan kasuwa ke yi na kara farashin kayan masarufi, ciki har da kayan abinci a farkon kowanne azumin Ramadan.

Wannan halin ya saba da watan Ramadan da kuma shari’ar musulunci.” Shugaba Buhari ya kara da cewa:

Advertisement

”Yayin gudanar da wannan muhimmiyar ibada a rayuwar musulmi, mu rabawa marasa karfi kayan abinci don su samu irin ni’imar da mu ke ciki, Allah ya na ninka ladan ayyukan alheri.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending