Sports
FIFA ta karbe daukar nauyin gasar kofin duniya daga Indonesia
Hukumar kwallon kafar duniya ta karbe damar daukar nauyin gasar cin kofin kwallon kafa ta matasa ‘yan kasa da shekaru 20 daga hannun Indonesia.
Matakin ya biyo bayan soke yin jadawalin gasar da aka shirya yi a Bali babban birnin kasar Juma’ar makon da ya gabata .
Hukumar kwallon kafar Indonesia ta ce ya zame wa Fifa dole ta soke yin wannan jadawali saboda yadda gwamnan Bali, Wayan Koster ya ki karbar tawagar kwallon kafar Isra’ila.
Daga ranar 20 ga watan Mayu zuwa 11 ga watan Yuni aka shirya gudanar da wannan gasa.
Indonesia ba ta da wata huldar diflomasiyya da Isra’ila, kuma a kwanakin baya ne wasu masu zanga zanga suka yi gangami, inda suka bukaci a dakatar da tawagar Isra’ila daga gasar don nuna goyon baya ga Falasdinawa.
A shekarar 2019 ce Indonesia ta samu damar daukar nauyin gasar, kafin ma Isra’ila ta samu tikitin shiga gasar.
Yanzu dole ne FIFA ta yi hanzari wajen samun kasar da za ta maye gurbin Indonesia wajen daukar nauyin gasar ta bana.
Fri
