News
Kiristoci a Uganda sun tsere zuwa Ethiopia saboda PASTO ya ce za ayi tashin kiyama kwanan nan
Dubban Kiristoci mabiya Cocin Chris Disciples Church (CDC), sun tsere daga ƙasar Uganda zuwa ƙasar Habasha domin tsira daga tashin alkiyama.
Mabiya COCIN dai sun yi imanin cewa za a fara tashin kiyama ne daga yanƙin su kuma ƙasa ɗaya ce a duniya za ta tsira ita ce ƙasar Ethiopia saboda haka suka tsere zuwa ƙasar domin tsira kamar yanda malamin cocin ya fada
Hukumomi a biranen Kampala da Adis Ababa sun tabbatar da faruwar lamarin, sai dai har yanzu ba akai ga tantance adadin yawan mutanen da suka tsere ba
Shugabannin COCIN Chris Disciples Church (CDC) dai sun shaidawa magoya bayan su cewa kwanan nan za ayi tashin kiyama kuma daga ƙasar UGANDA duniya za ta fara karewa inda kasar Habasha ne kawai za ta rage a fadin duniya.
GASKIYA TADI KWABO
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News2 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
