Connect with us

News

Hukumar NCC Tace Bata Bibiya Ko Amfani Da Muryoyin Kiran Wayar Kowa 

Published

on

Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta kasa NCC ta musanta zargin bin diddigin da daukar maganganu da tattaunawar da Mutane ke yi ta wayar tarho, inda ta ce ba ta kuma ba za ta iya aiwatar da hakan bisa doka.

 

Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar NCC, Reuben Muoka, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya bayyana cewa hukumar ta samu sakonni kan ikirarin da wasu mutane da kungiyoyi ke yi na bibiyarsu ta wayar tarho da kuma daukar maganganun inda batun ya haifar da musayar ra’ayoyi a a shafukan sada zumunta.

Advertisements
Advertisements

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Tabbatar Da Rahoton Yin Garkuwa Da ‘Daliban Makaranta

A cewar Muoka, hukumar ta musanta zargin tare da ayyana cewa ta kai rahoton zargin ga hukumomin tsaro da suka dace domin gudanar da bincike da kuma daukar matakin da ya dace.

Advertisements
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending