Connect with us

News

Hajjin Bana: Kano Ta Sa Ranar Rufe Karɓar Kuɗin Maniyyata

Published

on

 

Hukumar kula da alhazai ta jihar Kano ta yi kira ga maniyyata da suka kai kuɗin ajiya a wani ɓangare na zuwa hajjin bana, su kammala biyan kuɗinsu daga nan zuwa ranar 21 ga wannan wata.

Advertisement

Tun da farko, hukumar alhazan ta buƙaci maniyyatan su cika kuɗin tafiyarsu zuwa naira miliyan biyu da rabi kafin Hukumar kula da Aikin Hajji ta Najeriya ta sanar da haƙiƙanin farashi.

Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomin Najeriya (ALGON) Ta Gargadi Kwamitin Abba Kan Zafafa Siyasa

A ranar Juma’a ne, Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa ta sanar da kuɗin tafiya aikin hajjin bana, inda Kano ta faɗa cikin jihohin da za su biya N2,919,000.00.

Advertisement

Da yake jawabi ga manema labarai ranar Asabar, Babban Sakataren Hukumar Alhazai ta Kano, Alhaji Mohammad Abba Dambatta, ya ce nan ba da jimawa ba za a rufe karɓar kuɗin tafiya aikin hajjin.

Ya ce maniyyatan Kano za su biya sama da naira miliyan biyu da dubu ɗari tara ne saboda tashin farashin dalar Amurka da ƙarin haraji daga Saudiyya da kuma kamfanonin sufurin jiragen sama.

Advertisement

Danbatta ya kuma kara da cewa batun sake ginin masaukan alhazai a kasa mai tsarki da hukumomin kasar ke yi, don inganta Jin dadi da walwalar alhazai bakin Allah, shima ya haifar da tsadar kudin aikin Hajjin na bana.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending