News
Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomin Najeriya (ALGON) Ta Gargadi Kwamitin Abba Kan Zafafa Siyasa
Kungiyar Shugabannin Kananan Kwamitin Karbar Mulki na Jam’iyyar NNPP da ya daina zafafa siyasa da haifar da tashin hankali ko furta lafuzan da ka iya haifar da hargitsi.
Shugaban ALGON na jihar Kano, Bappa Muhammad ya yi kiran ne a sanarwa da ya fitar, kan zargin karkatar da kudaden al’umma da kwamitin ke yi wa shugab kananan hukumomin jihar domin bayar da tallafin karashen zaben da ke tafe nan gaba.
A cikin makon nan ne dai shugaban kwamitin, Abdullahi Baffa Bichi ya gargadi shugabannin kananan hukumomin kan yin almubazarranci da dukiyar gwamnati.
Amma a martaninta kungiyar ta yi kira gare shi da ya yi aiki da hankali domin irin wannan tashin hankalin jama’a ba zai iya tasowa ba a wannan tafiyar ta dimokuradiyya.
“An saba yin irin wadannan zarge-zargen a duk lokacin da aka samu sauyin a shugabanci.
“Muna so musamman mu tunatar da mai yin wadannan zarge-zarge game irin hakan da aka yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso a shekarar 2014 na yin amfani da kudaden al’umma da ya karbo daga kananan hukumomi 44 da aka yi wa shugaban kasa buri.
“Idan dai za a iya tunawa dai an yi zargin an karbo makudan kudade har Naira miliyan saba’in daga kowacce daga cikin kananan hukumomi 44 da ke jihar ba bisa ka’ida ba, wanda har yanzu shari’ar tana gaban hukumomi, ta ki da cin hanci da rashawa’’.
A ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa ne dai ake sa ran rantsar da Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin sabon gwamnan jihar Kano.
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News4 days ago
ICPC Ta Wanke Femi Gbajabiamila Daga Zargin Badakalar Hukumar Bogi
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Dakile Yunkurin Sace Jariri Da Wasu Ma’aikatan Asibiti A Jigawa
