Business
Kungiyar OPEC za ta yi taro don duba yiwuwar rage yawan man da take fitarwa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZHRADEEN
Ƙungiyar ƙasashe Masu Arzikin Man Fetur ta OPEC za ta gudanar da taro a yau Lahadi tare da ƙawayenta domin tattauna batun rage yawan man da ƙungiyar ke fitarawa zuwa kasuwannin duniya.
kungiyar ta shirya taron ne a daidai lokacin da farashin man ke faɗuwa a kasuwannin duniya sakamon matsin tattalin arziki da mafiya yawan ƙasashen duniya ke fuskanta, lamarin da ya haifar da rage yawan buƙatar man a ƙasashen.
Ministocin ƙasashe mambobin ƙungiyar 13 tare da ƙawayenta da Rasha za su gana a shalkwatar ƙungiyar da ke birnin Vienna domin tattaunawa game da batun.
A watan Afrilun da ya gabata ne ƙungiyar ta rage adadin man da take fitarwa zuwa kasuwannin duniya a wani mataki na farfado da farashin man a kasuwannain duniya.
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News4 days ago
ICPC Ta Wanke Femi Gbajabiamila Daga Zargin Badakalar Hukumar Bogi
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Dakile Yunkurin Sace Jariri Da Wasu Ma’aikatan Asibiti A Jigawa
