News
An yi gwanjon takalmin Michael Jordan kan Dala miliyan 2.2
A Talatar nan aka sayar da wasu takalman da fitaccen dan wasan kwallon kwando, Michael Jordan ya yi amfani da su, kan Dala miliyan 2 da dubu dari 2, wanda ya kafa tarihi a kasuwar gwanjon takalman da ‘yan wasa suka yi amfani da su wajen buga wasa.
Dan wasan kwallon kwando Jordan ya sanya takalmin ne yayin wasansu na karshe a gasar cin kofin NBA a shekarar 1998 wacce ita ce ta shida kuma ta karshe da ya lashe.
Cinikayyar da aka gudanar ta kafar Intanet ta tabbatar da matsayi da kuma tarihin da Jordan ya kafa a matsayin dan wasa mafi daraja da aka yi gwanjon kayansa da ya sanya yayin wasa.
Siyayyar dai ta karya tarihin da takalmansa suka kafa, wanda aka sayar kan Dala miliyan 1 da rabi, a watan Satumbar shekarar 2021.
Ko a shekarar da ta gabata sai da aka sayar da daya daga cikin rigarsa kan Dala miliyan 10 da dubu dari, wacce ita ta zamo gwanjon rigar wani dan wasa mafi tsada.
Kamfanin gwanjon ya ce, Jordan ya sanya hannu kan takalman sannan ya bai wa wani mai miko kwallo daga wajen fili bayan an tashi wasan.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News5 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
