News
Rashin wutar lantaki a kano ya rage walwalar jama’a a Ramadan
A yayin da ake fuskantar matukar zafin yanayi da kuma ibadar azumin watan Ramadan, yanzu haka jama’a na ci gaba da kokawa bisa rashin tsayuwar hasken lantarki a fadin jahar kano, lamarin rashin rashin wutar lantarkin ya jefa al’uma da dama cikin mawuyacin hali.
Duk da cewa ’kanawa sun samu ingancin wutar lantarki a ‘yan kwanakin da suka gabata, sai ga lamarin ya dagule a ‘yan kwanakin da muke ciki, inda aka fara fuskantar matsalar a lokacin zafi, lamarin da ya haifar da rashin walwala a tsakanin al’umma.
Majalisar Najeriya ta gayyaci ministoci kan bacewar gangunan danyen mai
Mazauna unguwa uku dake Tarauni local government a jihar kano sun yi matukar kokawa kan katsewar hasken latarkin musamman a a wannan watan na Ramadan
Wannan ya sanya mutane neman bayani dangane da halin kunci da suka samu kansu ciki daga kamfanonin da ke aikin rarraba wutar, sanadiyar rashin wutar.
Salim, wani mazaunin yankin Rogo local government ne a jihar kano ya baiyana cewa tun makon da ya gabata suka fara fuskantar matsalar wutar lantarkin.
Shi kuwa Abdullahi musa cewa ya yi makonni biyu rabonsu da samun wutar lantarki na tsawon sa’o’i uku a rana.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News5 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
